Home Labaru Sojoji Sun Fantsama Ofishin Ndlea Don Kubutar Da Wani Soja Da Aka...

Sojoji Sun Fantsama Ofishin Ndlea Don Kubutar Da Wani Soja Da Aka Kama Ya Na Maskewa

237
0

Wasu zaratan sojoji sun afka ofishin hukumar hana sha da
fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Jigawa, indaa su ka yi
kokarin fitar da wani soja da jami’an hukumar su ka kama a
wani samame da su ka kai dabar yan kwaya.

Wani mazaunin kusa da inda lamarin ya auku ya shaida wa manema labarai cewa, sojojin, wadanda yawan su ya kai 10 sun afka ofishin ne dauke da sanduna da karafuna domin su kubutar da dan’uwan su da ke tsare.

Jami’an hukumar NDLEA dai sun kama sojan ne, a wani wuri da ake harkallar miyagun kwayoyi tare da wasu abokan sa farar hula daidai lokacin da su ke sheke ayar su.

Rahotanni sun ce, mutane sun yi cincirindo a kofar ofishin NDLEA, lokacin da sojojin ke kokarin kubutar da abokin aikin su, sai dai kuma a dalilin haka ya sa su ka hakura su ka fice daga ofishin.

Leave a Reply