Home Labaru Sojin Najeriya Sun Kama Jagoran Ipob A Enugu

Sojin Najeriya Sun Kama Jagoran Ipob A Enugu

72
0

Dakarun runduna ta 82 ta sojojin Najeriya a Jihar Inugu sun kama Godwin Nnamdi, wani jagoran ƙungiyar ‘yan  ta’adda ta IPOB.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun rundunar Operation Golden Dawn ne suka kama wanda ake zargin a ranar Kirsimeti.

Janar Nwachukwu ya ce an kama gawurtaccen shugaban ƙungiyar yayin wani sintiri a Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.

Janar Nwachukwu ya ce Sojojin sun ƙwace bindiga kirar AK-47 da harsasai da kuma wayar salula daga hannun Godwin Nnamdi.

An kama jagoran IPOB ne dai yayin wani samame a wani sansani da ake zargin shi ne matsugunin ƙungiyar a Dajin Akpowfu da ke Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.