Home Home Sobon Rikicin Makiya Da Manoma Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 13 A...

Sobon Rikicin Makiya Da Manoma Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 13 A Filato

290
0

Akalla mutane 13 su ka rasa rayukan su a yankin karamar hukumar Barikin Ladi ta jahar Filato, a ci-gaba da kai wa juna harin ramuwar gayyar da ake yi tsakanin makiyaya da manoma.

Wannan dai ya na zuwa ne, kwana daya bayan an yi ma wasu makiyaya biyar kwanton bauna aka kashe su a garin Rawuru da ke karamar hukumar, inda sa’oi kadan bayan faruwan hakan wasu dauke da bindigogi su ka yi wa garin dirar mikiya su ka kashe mutane 8 nan take.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar DSP Alabo Alfred ya tabbatar da faruwar harin na biyu, sai dai ya ce ba ya da masaniyar kashe makiyayan da aka yi.

DSP Alabo, ya ce kawo yanzu ba su kammala tattara adadin mutanen da su ka mutu da yawan gidajen da aka kona ba.

Sai dai shugaban kungiyar Fulani makiyaya reshen jihar Filato Nuru Abdullahi ya tabbatar da kasin mutanen biyar da aka yi,  lokacin da su ka kai dabbobin su kasuwa domin saidawa a yankin Bukuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Leave a Reply