Home Labaru Siyasar Ghana: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Gangamin ‘Yan Adawa A Accra

Siyasar Ghana: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Gangamin ‘Yan Adawa A Accra

168
0

‘Yan sanda a birnin Accra na Ghana sun yi amfani da kulake da
barkonon tsohuwa wajen tarwatsa wasu darurruwan jama’ar
magoya bayan ‘yan adawa da suka yi zanga-zanga a kusa da
ginin hukumar zabe.

‘Yan adawar sun yi gangamin ne domin nuna kin amincewa da
sakamakon zaben da hukumar ta bayyana wanda ta
tabbatar cewa Nana Akufo Addo shi ne ya lashe zaben shugaban
kasar da aka gudanar a ranar tara ga watan Disamba, da kashi
51.59 a gaban dan takarar jam’iyyar adawa John Mahama da ke
dashi 47.36.

Jami’an tsaron na Ghana sun kama da yawa daga cikin
shugabannin adawar da suka jagoranci gangamin.