Home Home Siyasar 2023: Atiku Ya Gana Da Shugabannin CAN a Abuja

Siyasar 2023: Atiku Ya Gana Da Shugabannin CAN a Abuja

42
0

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Abuja.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa a Twitter, inda ya ce taron ya gudana ne a cibiyar Ecumenical da ke Abuja.

Akwanakin baya ne Atiku ya yi alkawarin tattaunawa da shugabannin CAN domin tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki wajen nema wa Najeriya mafita.

A baya dai shima Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya gana da shugabannin CAN, inda suka tattauna kan batun zabar musulmi da musulmi a 2023.

A yayin ganawar, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa idan aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, gwamnatinsa za ta yi tafiya da kowa ba tare da la’akari da bambancin addini ba.