Home Home Shugabancin Kano: Zan Binciki Bashin N241bn, Cewar Abba Kabir Ga Ganduje

Shugabancin Kano: Zan Binciki Bashin N241bn, Cewar Abba Kabir Ga Ganduje

81
0

Sabon Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin gudanar da bincike a kan bashin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo na Naira biliyan 241.

Gwamna Yusuf, ya ce takardun bayanan gwamnati da Ganduje ya miƙa ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar mai barin gado ba su wadatar ba.

Abba Gida-gida dai ya caccaki Ganduje a kan rashin tasayawa ya miƙa ragamar mulki da kan sa, amma ya wakilta wani maimakon haka.

Ya ce takardun bayanan gwamnatin sun yi mana kaɗan, kuma na kwamitin miƙa mulki ba su da yawa, ya na mai cewa babu abin da za su iya yi a matsayin su na wakilan jama’a, don haka ba za su ƙi karɓar abin da aka miƙa ma su ba.

Leave a Reply