Uwargidar shugaban ƙasa A’isha Buhari ta buƙaci shugabanni a arewa su yi koyi da na kudancin ƙasar nan wajen naɗa mata a muƙamin mataimakan gwamnoni.
Hajiya A’isha ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa ta kafar sada zumunta, inda ta ce naɗa matan a muƙamin zai taimaka wajen shigar da su a harkar siyasa.
Ta ƙara da cewa “wannan ce hanya mafi kyawu a ƙoƙarin ganin an yi adalci ta ɓangaren jinsi, a maimakon goyon bayan mutum guda mai neman nasara ko ta halin ƙaƙa.
A cikin sanarwar tata, A’isha Buhari ta kuma gode wa jagororin jam’iyyar APC na jihar Adamawa, inda rikici ya turnuƙe a kan takarar gwamnan jihar.
A makon da ya gabata ne kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Sanata A’isha Binani ce halastacciyar ƴar takarar gwamna, bayan wata kotun ta soke takarar.
You must log in to post a comment.