Home Labarai Shugaban Somaliya Ya Dakatar Da Firaminista

Shugaban Somaliya Ya Dakatar Da Firaminista

231
0

Shugaban kasar Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed ya sanar da dakatar da Firamistan kasar Mohammed Hussein Roble daga mukamin sa.

Dakatar da Firanministan dai ya biyo bayan musayar yawun tsakanin sa da shugaban kasa a ranar Lahadi, inda dukkan bangarorin biyu ke zargin juna kan sarkakiyar da ke tattare da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

A cikin sanarwar da offshin shugaban kasar ya fitar, ta ce Firaministan ba zai cigaba da rike madafun iko ba har sai an kammala bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma almubazarranci da dukiyar kasa.

Sanarwar ta kuma kara da cewa ‘yan majalisar ministocin za su cigaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda dokar kasa ta tanadar. 

Tun dai a safiyar ranar Lahadi ce offishin shugaban kasar ya zargi Roble da zama babban barazana ga shirye-shiryen zabe da kuma wuce makadi da rawa a harkokin tafiyar da mulkin sa.

Leave a Reply