Home Labaru Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidajen Yari

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidajen Yari

256
0
President Bola Tinubu
President Bola Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa Nwakuche Ndidi, a matsayin shugaban riƙo na hukumar kula da gidajen yari na ƙasa.

Cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar hukumar tsaro ta sibil difens da hukumar kashe gobara da ta shige da fice, Ja’afaru Ahmed ya ce naɗin Ndidi zai fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Disamban nan.

An haifi Nwakuche Ndidi ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 1966 a garin Oguta na jihar Imo.

Kafin naɗinsa kan muƙamin shi ne mataimakin shugaban hukumar mai lura da horaswa.

Naɗin nasa na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin shugaban hukumar na yanzu, Halliru Nababa.

A ranar 18 ga watan Fabrairu ne dai tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa Nababa a muƙamin.

Leave a Reply