Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna bacin rai kan kisan kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina Dakta Rabe Nasir.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar, Shugaba Buhari ya ce kisan kwamishinan mummunan abu ne kuma abin ayi tir ne, inda ya ƙara da cewa irin waɗannan mugan ayyukan ba su da mazauni a Najeriya.
Shugaban kasa ya kuma buƙaci jami’an tsaro su gudanar da bincike da kuma tabbatar da cewa an yi hukunci kan waɗanda aka kama da laifi.