Home Labaru Shugaba Buhari Ya Bukaci Gwamnoni Su Yi Koyi Da Matawalle Maradun

Shugaba Buhari Ya Bukaci Gwamnoni Su Yi Koyi Da Matawalle Maradun

1040
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya zama dole a rika jinjina wa gwamnan jihar Zamfara Dakta Bello Matawalle Maradun, saboda jajircewar da ya yi wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar Zamfara.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya karbi bakuncin sarakunan yankin Arewacin Nijeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja a karkashin jagorancin sarkin Musulmi Muhammad Abubakar III.

Shugaban Buhari, ya ce ya na kira ga gwamnatocin jihohin Nijeriya su yi koyi da Matawalle, bisa yadda ya maida hankali wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar sa. Haka kuma, shugaba Buhari ya kalubalanci sauran gwamnoni su lalubi irin matakan da Matawalle ya dauka har ya yi nasarar samar da zaman lafiya a jihar Zamfara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com