Home Labaru Shari’ar Atiku Da Buhari: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Ranar 13 Ga...

Shari’ar Atiku Da Buhari: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Ranar 13 Ga Satumba

473
0

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, ta shirya yanke hukunci tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP ranar 13 ga Satumba, 2019.

Sashe na 134 (1) da (3) na dokar zabe dai, ya ce za a iya shigar da kara a tattauna a kotu, sannan a yanke hukunci a cikin kwanaki 180 bayan zabe.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, za a yanke hukunci a kan karar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP su ka shigar kafin ranar 15 ga watan Satumba na shekara ta 2019.

A makon da ya gabata dai, kotu ta hana jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar duba rumbum hukumar zabe na adana sakamakon zabe a yanar gizo.