Home Labarai Sayen Kyamarorin Tsaro: Kotu Ta Janye Umarnin Hana Ganduje Ciwo Bashin Biliyan 10

Sayen Kyamarorin Tsaro: Kotu Ta Janye Umarnin Hana Ganduje Ciwo Bashin Biliyan 10

169
0

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta Janye umarninta na hana Gwamnatin Jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10 domin sanya kyamarorin tsaro na CCTV a jihar.


Da farko kotun ta hana gwamnatin karbo bashin ne, bayan karar da Kungiyar Kano First Forum (KFF) ta shigar tana kalubalantar gwamnatin, saboda saba ka’idojin karbar bashin.


Kungiyar ta hannun lauyanta, Barista Badamasi Sulaiman, ta bayyana shirin gwamnan jihar na ciyo bashin a matsayin haramtacce saboda ya saba da Dokar Karbar Bashi ta Ofishin Kula da Basussuka ta Shekarar 2003 da dokar Ma’aikatar Kasafin Kudi ta 2007 da kuma Dokar Karbar Bashi ta Jihar Kano ta 1968.


Amma lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Barista Muhammad Dahuru suka nemi kotun ta jingine wancan umarni na dakatarwar da ta yi tunda farko.


Alkallin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya bayyana cewa kotu tana da damar ta jingine umarnin da ta bayar bayan tsawon kwana 14.


Ya kuma umarci masu kara da su ci gaba da duba lamarin a gaban kotun Abuja saboda kotunsa za ta tafi hutu.

Leave a Reply