Shugaban Uganda Yoweri Museveni na zargin ƙasashen Yamma da baki biyu da kuma munafurci musamman idan ana batun sauyin yanayi.
A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Museveni ya bayar da misali da batun rushe wata cibiyar samar da lantarki ta hanyar iska a Jamus domin faɗaɗa wurin haƙar kwal.
Ya bayyana cewa wannan wani abin dariya ne ga ƙasashen idan ana batun cika alƙawuran sauyin yanayi.
Mista Moseveni ya ce ƙasashen Turai na jin daɗi su kwashe albarkatun ƙasashen Afrika domin amfanin makamashin su amma ba sa so a samu ci gaba a Afrika ta ɓangaren albarkatu irin su Fetur da kwal wanda mutanen Afrika ke amfana da su.
Ya ce ana sa ran nan da shekara uku Uganda za ta soma fitar da man fetur.
You must log in to post a comment.