Home Home Sauya Fasalin Kudi: Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar Da Sabbin Takardun Kudi Yau...

Sauya Fasalin Kudi: Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar Da Sabbin Takardun Kudi Yau Laraba

54
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi da aka sake wa fasali a yau Laraba.

Gwamnan babban bankin ƙasa CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a wajen taron kwamitin tsare-tsaren kuɗi.

Emefele ya ce babban bankin ƙasa ba zai sauya ranar ƙarshe da ya saka na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankunan domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.

Ya ƙara da cewa shugaban zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin a lokacin taron majalisar zartarwa na ƙasa.

Tun da a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin CBN ya sanar da cewa za a sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar nan.

Ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo ne daga ranar 15 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da kashe su tare da tsoffin kuɗin har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ƙudin.