Home Home Sau 98 Babban Layin Wuta Na Ƙasa Na Lalacewa Ƙarƙashin Mulkin Buhari

Sau 98 Babban Layin Wuta Na Ƙasa Na Lalacewa Ƙarƙashin Mulkin Buhari

90
0
Wasu bayanai daga kamfanonin rarraba wutar lantarki a Nijeriya sun nuna cewa, ƙarfin wutar lantarki ya ragu da megawatt 981.8 tsakanin shekara ta 2015 zuwa watan Agusta na shekara ta 2022, duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta zuba kudi sama da naira tiriliyan biyu a bangaren tun hawan Shugaba Buhari a shekara ta 2015.

Bayanan sun ce, babban layin wutar lantarki na Nijeriya ya dauke sau 98 a ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Haka kuma, bayanan kamfanonin sun nuna cewa, ƙarfin wutar lantarki ta Nijeriya ya na megawatt dubu 6 da 616.28 a shekara ta 2015, inda ya sauka zuwa megawatt dubu 5 da 634.47 a watan Agusta na wannan shekarar.

Wata majiya ta ce, rashin da aka yi a bangaren lantarki tsakanin shekara ta 2015 zuwa watan Agusta na shekara ta 2022 ya kai naira tiriliyan 1 da miliyan 76, inda masu gudanar da harkar ke nuna takaicin tabarbarewar al’amurra a bangaren tun bayan raba masana’antar a watan Nuwamba na shekara ta 2013.