Babbar Kotun Jihar Kano, ta ba lauyoyi umarnin daina hira da manema labarai kan shari’ar dambarwar Masarautar Kano.
A zaman kotun na ranar Alhamis ne Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta ba da umarnin.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, wadda ke sauraron shari’ar mai sarkakiya ta ce, tana umartar lauyoyi kada su yi hira da ’yan jarida kafin ko bayan hukuncin,
da ta yanke kan rokon da wanda ake kara na farko ya gabatar na neman dakatar da wannan shari’a.
Antoni-Janar na Jihar Kano da Majalisar Dokoki da shugaban ta ne suka shigar da kara gaban kotun.
Sun garzaya kotun ne ranar 27 ga watan Mayu 2013, suka nemi ta umarci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero,
da sauran sarakuna hudu da aka rushe masarautun su daga gabatar da kan su a matsayin sarakunan masarautun na Bichi, Gaya, Karaye, da Rano.
Wadanda ake kara su ne sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado-Bayero,
da Sarkin Karaye Dr Ibrahim Abubakar ll, da Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa, da kuma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya.
Sauran wadanda ake kara su ne Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, da Daraktan Hukumar Tsaro ta DSSn a Jihar Kano, da Kwamandan Sibil Difens na jihar da kuma Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya.














































