Home Labaru Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Ƙi Amincewa Da Sanata Akpabio

Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Ƙi Amincewa Da Sanata Akpabio

310
0

Sanatocin da za su kammala wa’adin su da zaɓaɓɓun da za su
hau daga yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, sun ce ba su
ba za su amince da Sanata Godswill Akpabio ya zama
Shugaban Majalisar Dattawa ba.

‘Yan majalisar, sun ce buƙatar su ita ce shugaban majalisar dattawa ya fito daga yankin Kudu maso Gabas ba Kudu maso Kudu inda Sanata Akpabio ya fito ba.

Sanatocin sun bayyana wannan matsayar su ne, yayin wani taron gaugawa da su ka gudanar a Abuja.

Idan dai ba a manta ba, Gwamna Ganduje na jihar Kano ya ce Gwamnonin APC sun yanke shawarar cewa Godswill Akpabio ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa, lamarin da ya sa Sanata David Umahi daga jihar Ebonyi ya janye daga takarar bayan Tinubu ya roƙe shi ya janye.

Leave a Reply