Home Labaru Samun ‘Yancin Kai: Jamhuriyar Nijar Na Bikin Cika Shekaru 59

Samun ‘Yancin Kai: Jamhuriyar Nijar Na Bikin Cika Shekaru 59

398
0

A yau Asabar 3 ga watan Agusta ne kasar Nijar ta yi bikin cika shekaru 59 da samun ‘yancin kai daga Faransa da ta yi mata mulkin mallaka.

Bikin a wannan karon ya zo ne a dai dai lokacin da matsalolin tsaro suka dabaibaye kasar, musamman hare-haren kungiyoyin ta’addanci.

Kamar yadda aka saba bisa al’ada shugaban kasar ta Nijar na gabatar da jawabi ga al’umma game da halin da kasar ke ciki a jajiberan wannan rana, kuma a wannan karon ma haka abin ya faru inda shugaba Mahamadou Issoufu, ya gabatar da jawabi kan batutuwa daban-daban.

Yayin jawabin shugaba Mahamadou Issoufou gabanin fara taron bikin ranar gadan-gadan, ya yaba da nasarar da aka samu ta fuskar yaki da ta’addanci a kasar, wanda ya ce na da nasaba da tallafin dakarun ketare da kasar ke samu.

Kai tsaye shugaban na Nijar, baya ga jinjinawa dakarun Sojin kasar ya kuma yaba da kokarin dakarun rundunar Barkhane baya ga Sojin Amurka wadanda ya ce suna taimakawa matuka wajen kakkabe ayyukan ta’addanci a Nijar.

A dai irin wannan rana ta 3 ga watan kowanne Agusta da Nijar kan tuna da ranar ‘yanci, hukumomi da manyan jami’an gwamnati kan yi amfani da damar wajen dashen itace da nufin magance matsalar kwararowar hamada.

Leave a Reply