Home Labaru Samun ‘Yanci: An Sako Ɗalibai 32 Na Sakandaren Bethel Baptist Ta Kaduna

Samun ‘Yanci: An Sako Ɗalibai 32 Na Sakandaren Bethel Baptist Ta Kaduna

64
0
Daliban Kaduna

Rahotanni na cewa ‘yan bindiga sun saki ƙarin dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna.

Wani mahaifi da BBC Hausa ta zanta da shi ya ce sun karɓo ya’yan na su bayan biyan kudin fansa, amma har yanzu ‘yan bindigar na rike da ƙarin ɗaliban 31, ya kuma ce tuni an haɗa daliban da iyayen su.

Sakin daliban Bethel Baptist na zuwa kwana ɗaya bayan sakin ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina a Jihar Naija bayan shafe kwana 88 a hannun ‘yan fashin daji.

A ranar 5 ga watan Yuli ne ‘yan bindigar suka kutsa makarantar Bethel Baptist da ke kan titin Kafanchan zuwa Kaduna, inda suka sace ɗalibai 121.

‘Yan fashin sun sako 28 daga cikin su a ranar 25 ga Yuli bayan an biya kuɗin fansa.

Kazalika, sun sake sako ƙarin 15 a ranar 22