Home Labaru Samar Da Ruga: Gwamnonin Arewa Sun Dauki Matakin Kebe Dabbobi A Gandu

Samar Da Ruga: Gwamnonin Arewa Sun Dauki Matakin Kebe Dabbobi A Gandu

293
0
Gwamnatocin Jihohin Arewa
Gwamnatocin Jihohin Arewa

Gwamnatocin jihohin Arewa sun yanke shawarar rungumar shirin gwamnatin tarayya na inganta harkokin kiwo ta hanyar kebe dabbobi a gandu.

Gwmanonin sun ce sun yanke wannan shawarar ce sakamakon yakinin da suke da shi cewa sabon tsarin zai kyautata zamantakewa tsakanin makiyaya da manoma, tare da bunkasa tattalin arzikin yankin.

Jihohi bakwai ne suka rungumi tsari ciki kuma har da jihar Filato, da Neja da kuma Nasarawa.

Sun ce tsarin wanda zai samar da makarantu da asibitoci da kuma ruwan da za su shayar da dabbobin su, kana  hanya ce ta magance rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya.

Gwamnonin sun ce ba wai fulani makiyaya ne kawai za su ci gajiyar tsarin rugar ba, duk wani mai sana’ar dabbobi zai amfana da shi.

A baya dai daman gwamnatin tarayya ta ce babu wata jihar da ta yi wa dole ta samar da Rugage domin killace dabbobin makiyaya kamar yadda wasu ke rade-radi.