Home Labaru Samar Da Mafita: Majalisar Amintattu Ta Ce Ɗaukar Matakan Shari’a Da Gangan...

Samar Da Mafita: Majalisar Amintattu Ta Ce Ɗaukar Matakan Shari’a Da Gangan Ne Ke Ɓata Sha’Anin Jagoranci A PDP

116
0
Wabara
Wabara

Majalisar Amintattu ta jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa akwai wasu ‘yan jam’iyyar da ke yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar zagon ƙasa ta hanyar ɗaukar matakan shari’a ga shugaba da sakataren jam’iyyar.

Shugaban kwmaitin, Sanata Adolphus Wabara ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron majalisar gudanarwar jam’iyyar da ake yi a Abuja.

Sanata Wabara ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ke damun ‘yan jam’iyyar shi ne  halin da shugabancin jam’iyyar ke ciki a yanzu haka.

Batun jagorancin jam’iyyar ne dai yake kokarin raba kan jama’a, inda ko a ranar Laraba sai da wani ɓangare na ‘yan jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga a sakatariyar jam’iyyar.

Leave a Reply