Home Labaru Sallar Idi: Gwamnati Ta Bayyana 25 Da 26 Ga Watan Mayu A...

Sallar Idi: Gwamnati Ta Bayyana 25 Da 26 Ga Watan Mayu A Matsayin Ranakun Hutu

456
0
Gwamnati Ba Ta Cire Dokar Hana Zirga-Zirga A Tsakanin Jihohi Ba
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin sake gina makarantun da Boko Haram su ka ragargaza a Jihar Yobe da sauran sassan jihohin Arewa maso Gabas.

Gwamnatin tarayya ta sanar da Litinin 25 da Talata 26 ga watan Mayun 2020 a matsayin ranakun hutun karamar sallah.

Ministan kula da harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyyana haka a wani jawabi da ya fitar a madadin shugaban kasa, sannan ya taya daukacin musulman Nijeriya murnar kammala azumin watan Ramadana.

Aregbesola ya kuma yi kira ga Musulmai su yi koyi da halayen Manzon Allah S.A.W, musamman hakuri da kaunar juna da kuma zaman lafiya.

Haka kuma, ministan ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta damu bisa yawaitar rikicin kabilancin a arewacin Nijeriya, lamarin da yasa ya yi kira ga al’umma su rika kallon kan su a matsayin ‘yan uwa.

Rauf Aregbesola ya sake jaddadawa bukatar gwamnatin Buhari na kokarin kawo karshen annobar COVID-19, da ayyukan ta’addanci, da kuma hada al’ummar kasa a matsayin tsintsiya madaurin daya.

Leave a Reply