Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Robbert Kennedy JR a matsayin sakataren lafiya na ƙasar.
Mukamin da ya Robert Kennedy Junior wani abu ne da zai janyo rarrabuwar kai tsakanin ‘yan majalisa musamman na adawa.
A jawabin da ya yi daga wurin shakatawa na Mar-a-lago, Mr Trump ya yaba wa Mr Kennedy, inda ya ce babu wanda zai iya aikin inganta fannin lafiya a Amurka kamar shi.
Kennedy mutum ne mai janyo cece-kuce kan allurar riga-kafi, musamman ra’ayin sa na nuna shakku kan riga-kafi lokacin annobar Korona.