Home Labarai Sabon Gwamna Da Aka Zaɓa A Ekiti Ya Ziyarci Buhari

Sabon Gwamna Da Aka Zaɓa A Ekiti Ya Ziyarci Buhari

21
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakwacin sabon gwamnan jihar Ekiti Biodun Oyebanji a fadar sa da ke Abuja.

Zababben gwamnan ya ziyarci shugaba Buhari ne bisa da rakiyar wasu gwamnoni da ‘yan Jam’iyyar APC da su ka taimaka wajen kai wa ga nasarar sa.

A ranar Asabar da ta gabata ne, hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa ta bayyana Biodun Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Ekiti.

Biodun Oyebanji dai yay i nasara a zaben ne da kuri’u dubu 178 da 57, yayin da dan takarar jam’iyyar SDP Olusegun Oni ya zo na biyu da kuri’u dubu 82 da 211, sai kuma Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP da ya zo na uku da kuri’u dubu 67 da 457.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa, jam’iyyar APC ce ta lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar, inda jam’iyyar PDP ta yi nasara a karamar hukuma daya kacal.