Home Labarai SABBIN TAKARDUN NAIRA: KUNGIYAR GWAMNONI TA NEMI A TSAWAITA WA’ADI NA SHEKARA...

SABBIN TAKARDUN NAIRA: KUNGIYAR GWAMNONI TA NEMI A TSAWAITA WA’ADI NA SHEKARA GUDA

36
0

Rikita rikitar canjin takardun kudi na naira ta dau wani sabon salo, bayan da kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta bukaci a tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin zuwa shekara guda daga yanzu.

Gwamnonin Jihohin Najeriyan 36 sun ba Babban Bankin Najeriya CBN shawarar ya kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin naira zuwa shekara daya nan gaba, a daidai lokacin da wasu Jihohi da kananan hukumomi suke karbar tsofin kudin, bayan kwararru a fannin tattalin arziki na ganin kara wa’adin shi ne mafi dacewa a halin yanzu.

Mai magana da yawun Kungiyar, Abdulrazak Bello Barkindo, ya shaida wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa wannan shawarar da Kungiyar Gwamnonin Najeriyan ta bayar ta biyo bayan wani zama na musamman ne da ta yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abdurrazak Bello, ya ce Gwamnonin sun nuna rashin jin dadin su da irin wahalhalun da ‘yan kasa ke fuskanta, inda suka ce duk da tabbacin da Ministan Shari’a ya bayar cewa Gwamnati za ta bi umurnin Kotun Koli al’amarin sai kara tsannanta ya ke, saboda haka suna ganin gara a dauki mataki na gaggawa saboda kar a yi wa tattalin arzikin kasa illar da ba za a iya jurewa ba.