Home Labaru Kasuwanci Sabani: Kamfanin China Ya Ƙwace Jirgin Najeriya Na 4 A Kanada

Sabani: Kamfanin China Ya Ƙwace Jirgin Najeriya Na 4 A Kanada

252
0
jet 1
jet 1

Kamfanin nan da ya ƙwace jiragen saman Fadar Shugaban Najeriya guda uku a ƙasar Faransa, ya sake ƙwace wani jirgin a Kanada.

Kamfanin Zhongshang Fucheng Industrial Investment Ltd,  ya ƙwace jiragen Najeriya da wasu kadarorin ta a wasu ƙasashe ne sakamakon rikicin da ke tsakanin sa da Gwamnatin Jihar Ogun.

A kwanakin baya ne Zhongshang Fucheng ya ƙwace jiragen Fadar Shugaban Ƙasa a Faransa bayan wata kotu da ke can ta ba shi nasara bayan sauraron ƙarar da ya shigar kan lamarin.

Daga baya  Zhongshang Fucheng ya saki ɗaya daga cikin jiragen fadar shugaban ƙasan Najeriyan a matsayin abin da ya kira ƙaramci,

sakamakon ganawar da aka shirya tsakanin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da takwaran sa na Faransa, Emmanuel Macron.

A kwanan kuma Zhongshang Fucheng ya samu sahalewar wata kotu na karɓar takardun mallakar wani ƙarin jirgin Najeriya ƙirar Bombardier 6000 daga hukumomin ƙasar Kanada.

Wata kotu ce da ke zamanta a  Quebec ce ta ba Zhongshang izinin ƙwace jirgin daga hannun Najeriya bayar sauraron shari’ar da kamfanin ke neman diyyar Dala miliyan 70 daga gwamnatin Najeriya.

Zhongshang ya ƙwace kadarorin Najeriya da dama a ƙasashen waje, baya ga jiragen sama da suka haɗa da Dassault Falcon 7X a birin Paris na ƙasar Faransa;

Boeing 737; Airbus A330 da kuɗin ya kai Dala miliyan 100; sai kuma Bombardier 6000 da yanzu kamfanin ya ƙwace a ƙasar Kanada.

Leave a Reply