Rundunar sojin Nijeriya, ta fitar da jerin sunayen mutane 50
da za ta yi wa karin girma, lamarin da ke zuwa a dai-dai
lokacin da ake sa ran wasu daga cikin manyan jami’an sojin
za su yi ritaya.
Sojojin 50 da aka fitar da jerin sunayen su domin yi masu karin girma, sun hadar na ruwa da sama da kuma na kasa, yayin da su ka ce nan ba da jimawa ba za a tabbatar da karin girman.
Rahotanni sun ce, za a kai mutanen zuwa mukaman Brigediya Janar da Kanar, inda za su maye guraben manyan sojojin da za su ajiye aikin su.
Duk da cewa majalisar gudanarwa ta rundunar sojin ba ta sanar da karin girman a hukumance ba, amma wadanda za a yi wa karin girman sun fito ne daga cikin kananan hafsoshin da aka yaye a rukuni na 43 daga kwalejin horar da kananan hafsoshin soji da kuma na rukunin 38 da 39.