Home Labarai Rundunar MNJTF Ta Ce Ƴan Boko Haram 263 Sun Ajiye Makamai

Rundunar MNJTF Ta Ce Ƴan Boko Haram 263 Sun Ajiye Makamai

119
0
0ffe854862b63cee722d4cce0ac8079623d94b376d8d7e06cfcd2322d45235cd
0ffe854862b63cee722d4cce0ac8079623d94b376d8d7e06cfcd2322d45235cd

Rundunar Sojojin Haɗin Gwiwwa mai Yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi ta ce mayaƙan ƙungiyar tare da iyalan su kusan 263 ne suka miƙa wuya ga sojojin .

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar,

ya ce ‘yan ƙungiyar sun fara rububin miƙa wuyar ne daga ranar 11 ga wtan Yulin, lokacin da wasu mutum biyar suka miƙa wuya ga sojoji a garin Wulgo da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Snarawar ta ce a ranar ne kuma, wasu ‘yan ƙungiyar 19 suka miƙa wuya a wani ƙauye da ke yankin Arewa Mai Nisa a Jamhuriyar Kamaru,

sannan cikin waɗanda suka miƙa wuyar akwai mata da ƙananan yara da kuma matasa.

Sojojin sun ce a ranar 15 ga watan na Yuli wasu ƙarin mutum 102, da suka haɗa da matasa 20 da mata 40 da ƙananan yara 42 ne suka miƙa wuya a yankin na Arewa mai nisa.

Kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske binciken farko ya gano cewa waɗanda suka miƙa wuyan ‘yan Najeriya da Kamaru ne,

tana mai cewa an miƙa ‘yan Najeriyar daga cikin su a hannun sojojin rundunar Operation HADIN KAI, domin ɗaukar mataki na gaba.

Leave a Reply