Home Home Rikicin Siyasa: ‘Yan Majalisa Sun Bai Wa Hammata Iska a Saliyo Kan...

Rikicin Siyasa: ‘Yan Majalisa Sun Bai Wa Hammata Iska a Saliyo Kan Dokar Zaɓe

37
0

Saɓani a kan wata sabuwar dokar zaɓe a Saliyo ya haddasa faɗa a tsakanin ‘yan majalisar dokokin kasar, inda suka riƙa bai wa hammata iska a zauren majalisar.

Abin da masu amfani da shafin twitter ‘yan saliyo suka kira hatsaniya an ga yadda ake ta kutufar juna a zauren majalisar.

An rika wurgi da sandar iko ta majalisar daga nan zuwa can.

Wani ɗan jarida ya ce daga nan ne kuma sai jami’an tsaro suka shiga tsakani inda suka yi waje road da wasu daga cikin ‘yan majalisar.

Rikicin ya barke ne tsakanin ‘yan majalisar jam’iyya mai mulki da kuma na jam’iyyun hamayya a kan wani kuduri na sanya wakilci a hukumar zaɓen kasar daidai da karfin kowace jam’iyya a kan shirin zaɓukan da za a yi a shekara mai zuwa.