Home Home Rikicin PDP: Atiku Ya Karbi Tayin Zaman Sulhun Da Bangaren Wike

Rikicin PDP: Atiku Ya Karbi Tayin Zaman Sulhun Da Bangaren Wike

48
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya amince da tayin neman yin sulhu da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da magoya bayan sa su ka nema.

Atiku ya kuma nuna cewa ya amince da sasantawa da su Wike ɗin domin a kawo ƙarshen rikici da dambarwar da su ka dabaibaye PDP.

Ya ce yin hakan abu ne mai muhimmancin da zai ƙara haɗa kan ‘yan jam’iyya, sannan ya ƙara ƙarfafa PDP ƙwarai da gaske.

Atiku ya yi tsinkayen cewa tun da aka fara wannan dambarwa da Wike da ‘yan ɓangaren sa, bai taɓa rufe masu ƙofar shiga a sasanta ba.

Daga nan ya yi kira ga dukkan shugabannin jam’iyya da magoya bayan ta su kasance masu goyon bayan wannan ƙoƙarin sasanci.

Wike da wasu gwamnoni huɗu sun janye daga shiga ko goyon bayan takarar shugabancin ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, har sai an biya masu buƙatar cire Shugaban PDP Iyorchia Ayu, an maye gurbin sa da ɗan Yankin Kudu tukunna.

Sun kuma nuna rashin amincewa da fitowar ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iyya daga ɓangare ɗaya, wato Arewa.