Home Labaru Rikicin Kaduna: An Sa Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomin Jema’a Da...

Rikicin Kaduna: An Sa Dokar Hana Fita A Ƙananan Hukumomin Jema’a Da Ƙaura

306
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a ƙananan hukumomin Jema’a da Kaura.

Tun farko dai an sanya irin wannan dokar a ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf domin daƙile rikicin da ke faruwa a yankin.

A daren Juma’ar da ta gabata ne gwamnan ya bayyana hakan, bayan wani hari da ‘yan bindiga su ka kai a wasu yankunan Jema’a da Marabar Kagoro duk a ƙaramar hukumar ƙaura ta jihar Kaduna.

A cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafin san a Twitter, El-Rufa’I ya ce tun a shekara ta 2017 aka ƙara kai jami’an tsaro kudancin Kaduna, bayan an gina wani sansanin sojoji a Kafanchan.