Home Home Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau Ya Yi Fatali Da Sulhun Uwar Jam’Iyyar Kan...

Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau Ya Yi Fatali Da Sulhun Uwar Jam’Iyyar Kan Rikicin Kano

204
0

Rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Kano na ƙara daukar sabon salo bayan ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sanarwar uwar jam’iyya kan sulhunta rikicin ‘ya’yanta na jihar.

Matsayar tsagin Sanata Shekarau da ya zabi Alhaji Haruna Dan-Zago a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano na da alaƙa da bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar.

A wata da yayi da manema labarai yi jim kadan bayan fitowar sanarwar jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.

Sanata Shekarau ya kara da cewa, sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da ɓangarorin biyu suka bukata ba.

Abu na biyu kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar ɗaya bangaren, sai da aka kai wa gwamna Ganduje takardar wadda kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam’iyyar, ko hedikwatar jam’iyya, da gwamna da kuma ni shugaban ɗayan barin jam’iyyar.