Home Labarai Rikici Na Kara Kazanta Tsakanin Armenia Da Azerbaijan

Rikici Na Kara Kazanta Tsakanin Armenia Da Azerbaijan

55
0

Mataimakin ministan harkokin wajen Armenia Paruyr Hovhannisyan, ya ce a bayyane ta ke karara taho mu gama tsakanin sojin kasarsa da na Azerbaijan na dada muni, wanda hakan ka iya maida su filin yaki gadan gadan.

Ma’aikatar tsaron Armenia ta ce sojojin Azerbaijan sun cigaba da luguden wuta tun da sanyin safiyar yau tsakanin iyakokin kasashen biyu.

Tun da fari Armenia ta zargi Azerbaijan da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma shekaru biyu da suka gabata.

Yaki ya barke tsakanin makwabtan biyu a shekarar 2020, lokacin da Azerbaijan ta mamaye kaso biyu cikin uku na yankin Nagorno-Karabakh, wanda ‘yan awaren Armenia ke iko da shi tun shekarun 1990.

A ranar Litinin rahotanni suka ce an kashe sojoji sama da 100 tsakanin kasashen biyu.

A cewar Firanministan Armenia Nikol Pashinyan an kashe sojojinsa 49 a dare guda, yayin da ma’aikatar tsaron Azerbaijan ta ce itama ta rasa sojoji 50.

To amma a ranar Talata Rasha ta ce ta shiga tsakani kuma an tsagaita wuta a rikicin na baya bayan nan.