Home Labaru Kasuwanci Raya Kasa: Mun Fidda Mutum Milyan 10 Daga Cikin Talauci A Shekaru...

Raya Kasa: Mun Fidda Mutum Milyan 10 Daga Cikin Talauci A Shekaru Shida

57
0

Gwamnatin tarayya ta fidda sama da yan Najeriya milyan 10 daga cikin bakin talauci ta shirye-shiryen tallafi da jin kai ta NSIP, a cewar Minista Sadiya Farouq. Hajiya Sadiya Umar Farouq, wacce take rike da kujerar Ministar Jin Kai da agaji, ta sanar da hakan ne a taron lissafin adadin mutanen dake fama da talauci a kasashe masu tasowa.

Ministar Jin Kai da agaji, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ’yan Najeriya miliyan 11 ne ya zuwa yanzu, suka ci gajiyar Shirin Tallafa wa da Ci gaban Al’umma (CSDP) a jihohi 29 inda aka kashe Dala miliyan 415 a kai.

Ta bayyana cewa ta hanyar shirin an gina azuzuwa guda 5,764 da cibiyoyin kiwon lafiya guda 1,323 a wasu kananan ayyuka guda 4,442 inda wasun aka yi musu kwaskwarima yayin da aka gudanar da wasu kananan ayyukan guda 16,166 a kauyuka 5,664.

Ministan ta fadi hakan a ranar Laraba a Abuja yayin wani taro kan shirin na CSDP, inda ta ce an faro shirin ne tun a 2009, sannan ya kunshi harkokin rayuwar yau da kullum guda takwas — ilimi da kiwon lafiya da ruwa da sufuri da lantarki da zamantakewar yau da kullum da muhalli da raya karkara.