Home Labaru Tsaro An Tsinci Gawar Wani Fasto Da Aka Kashe A Zangon Kataf

An Tsinci Gawar Wani Fasto Da Aka Kashe A Zangon Kataf

15
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanar da kisan Raberan Silas Yakubu Ali, wanda Fasto ne a cocin ECWA da ke Kibori Asha-Awuce da ke a karamar hukumar zangon kataf.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya ce an samu gawar faston ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a Kibori.

A wata sanarwa da aka fitar, ta bayyana cewa Raberan Ali ya je Kafanchan ne a ranar Asabar da ta gabata, amma daga nan ba a sake jin duriyar sa ba.

Sanarwar ta cigaba da cewa, yanzu haka jami’an tsaro na ci-gaba da gudanar da bincike domin gano masu hannu a kisan.