Home Labaru Rashin Kudi Ya Sa MDD Dakatar Da Tallafin Abinci A Yemen

Rashin Kudi Ya Sa MDD Dakatar Da Tallafin Abinci A Yemen

38
0

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rashin kuɗi ya tilasta masa daina kai agaji ga mutanen da ke cikin yunwa a Yemen.

Hukumar ta ce dole ne ta rage yawan agajin abincin da take bai wa ƴan Yemen miliyan takwas daga watan gobe.

Ta ce mutum miliyan biyar da ke cikin haɗarin fuskantar matsananciyar yunwa za su ci gaba da samun cikakken agaji, sai dai abincin da ke rumbunta ya yi ƙasa sosai kuma nan ba da jimawa ba dole a sake rage yawan agajin abincin.

Sama da ‘yan Yemen miliyan 11 ne ke tsananin bukatar agaji, ya yin da a yanzu su ke cikin barazanar mutuwa saboda annobar cutar korona.

Mummunann yakin da kawancen Saudiyya da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da kasashen yamma suka aminta da su, tsakaninsu da ‘yan tawayen Houthi shi ya janyowa kasar fadawa cikin mawuyacin hali.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce miliyoyin ‘yan kasar ne ke gudun hijira wasu kasashe, ya yin da mata da kananan yara da tsofaffi suka fi kowa shan wuya a wannan lokacin.