‘Yan kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, a Jami’ar Tarayya ta Gashu’a, a Jihar Yobe, sun gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin biyan su albashi.
Shugaban reshen, Dakta Melemi Abatcha, ta ce zanga-zangar na nuna adawa da yadda ake musguna wa malamai ta hanyar jefa su cikin kangin yunwa.
Melemi Abatcha ta jaddada cewa, maimakon magance manyan bukatu da kungiyar ta gabatar, gwamnatin tarayya ta hanyar hukumominta, ta yi amfani da kalaman batanci da kuma tsoratarwa, inda ta kara da cewa irin wadannan zarge-zarge na cin karensu babu babbaka ta hanyar kin biyansu albashin watan Oktoba.
A yayin da ta ke kira ga gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyar da suka kulla tare da biyan duk wani albashin su, shugabar ASUU ta ci gaba da cewa kungiyar ta yi watsi da wulakanci da ake yi wa malaman jami’o’in Nijeriya.
An ga ‘ya’yan kungiyar dauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban inda suka dinga zagaye jami’ar suna nuna rashin jin dadin su.