Home Labarai Rashi: Kashim Shattima Ya Halarci Jana’idar Kwamishina A Borno

Rashi: Kashim Shattima Ya Halarci Jana’idar Kwamishina A Borno

66
0
IMG 20240827 WA0000
IMG 20240827 WA0000

Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya halarci jana’izar, Kwamishinan kuɗi da ci gaban tattalin arziƙi na Jihar Borno, Alhaji Ahmed Ali Ahmed, tare da Gwamna Babagana Umara Zulum.

Jana’izar ta gudana ne a ranar Litinin a Maiduguri.

Babban limamin Borno, Imam Laisu Ibrahim ne, ya jagoranci sallar jana’iza.

Ahmed, ya rasu a gidansa da ke Maiduguri, kuma yana da shekara 42 a duniya.

Ya bar mata da yara biyu, da ’yan uwa da dama.

Kafin rasuwarsa, shi ne kwamishinan kuɗi da ci gaban tattalin arziƙi na Jihar Borno.

Ya yi aiki da bankin Zenith Bank sama da shekara 17, inda ya kai matsayin Mataimakin Manaja kafin shiga siyasa.

Jama’ar da suka halarci jana’izar sun haɗa da Mataimakin Shugaban APC, Ali Bukar Dalori, Sanata Kaka Shehu Lawan, ’Yan Majalisar Wakilai, Shugaban APC na Jihar Borno, Bello Ayuba, da ’Yan Majalisar Dokoki na Jihar.

Leave a Reply