Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce akwai babban aiki a gaba kafin dimokuraɗiyyar Nijeriya ta samu ci-gaban da ya kamata.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin saƙon sa na Ranar Demokradiyya, inda ya ce kamata ya yi ‘yan Nijeriyar da su ka shaida mulkin soja su yaba da samun dimokuraɗiyya a matsayin tsarin mulkin ƙasa.
Atiku Abubakar, ya ce dimokraɗiyyar da za a yi ba tare da bin dokokin da aka shimfiɗa ba daga ɓangaren masu ruwa da tsaki ba, hakan zai zama babu wani bambanci da mulkin soja. Ya ce “kafin dimokuraɗiyyar ta samu irin cigaban da ya dace, dole a sauka daga tsarin da ake gudanar da ita a yanzu, inda masu riƙe da madafun iko ke ayyana sakamakon zaɓe