Home Labaru Ramako: China Ta Karbe Ikon Ofishin Jakadancin Amurka Dake Chengdu

Ramako: China Ta Karbe Ikon Ofishin Jakadancin Amurka Dake Chengdu

195
0
Ramako: China Ta Karbe Ikon Ofishin Jakadancin Amurka Dake Chengdu
Ramako: China Ta Karbe Ikon Ofishin Jakadancin Amurka Dake Chengdu

Gwamnatin China tace jami’an ta sun karbe iko da ofishin Jakadancin Amurka dake Chengdu a yau Litinin, bayan ta bukaci rufe shi a matsayin ramako kan yadda Amurkar ta rufe mata nata ofishin a Houston.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta sanar da cewar da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin agogon kasar an rufe ofishin Jakadancin, kana daga bisani jami’an Chinan suka shiga ciki domin karbe iko da shi.

Da farko kasar Amurkan ce ta fara kulle ofishin jakadancin ta da ke birnin Houston bayan zargin kasar China da amfani da Ofishin a fakaice wajen aikata leken asiri, zargin da kai tsaye ke kara tsananta tsamin alakar da ke tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a Duniya.