Home Labaru Rabon N8,000 Duk Buge Ce” Inji Gwamnan Kaduna – Uba Sani

Rabon N8,000 Duk Buge Ce” Inji Gwamnan Kaduna – Uba Sani

80
0

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, ya bayyana shirin
bada tallafin kudi na gwamnatin tarayya a karkashin
jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin
yaudara.

Gwamnatin Tinubu dai ta bada shawarar raba wa iyalai miliyan 12 Naira dubu 8 na tsawon watanni shida, domin rage masu radadin cire tallafin man fetur da aka yi, shirin da aka jingine daga baya bayan ya sha suka daga yan Nijeriya.

Da ya ke magana a wata hira da gidan Talabijin Arise, Uba Sani ya ce babu wani sahihin bayani na wadanda za su amfana da shirin.

Gwamna Uba Sani, ya ce shi a ra’auyin sa ya na ganin shirin raba tallafin damfara ce da kuma Yaudara.

Sai dai ya ce ya kamata gwamnati ta fara tabbatar da ganin cewa an kula da mutanen da aka tsame daga cikin shirin kudin, musamman a arewa maso yamma sannan a kawo tsarin kudi kafin aiwatar da shirin bada tallafin kudin.

Leave a Reply