Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ɗan majalisar dattawa Ibrahim Shekarau, ya ce Najeriya ba ta bukatar majalisar dattawa da ta wakilai, kasancewar aiki iri ɗaya suke yi.
Shekarau, ya ce a nasa ra’ayin, ɓata kudi ne kawai gwamnati ke yi wajen tafiyar da majalisun dokokin biyu.
A tattaunawarsa da BBC, Shekarau ya ce kamata ya yi Najeriya ta rungumi tsarin mulki irin na Birtaniya, wanda aikin ƴan majalisar bai wuce na wucin-gadi ba.
Sai dai ya ce gyaran irin tsarin na majalisar dokoki a Najeriya abu ne mai matuƙar wahala domin sai an yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasa.
A cewar sa, akwai yiwuwar ƴan majalisar dokokin, waɗanda dole ne sai an samu amincewar su kafin a iya sauya dokar, ba za su goyi bayan canzawa ba.
Najeriya na da zauruka biyu ne na majalisun dokoki na tarayya, wadda ta haɗa da Majalisar Dattawa mai wakilai 109, sai kuma majalisar wakilan wadda take da wakilai 360.














































