Home Labaru Raɗɗa Ya Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da UNDP Don Inganta Tsaro A...

Raɗɗa Ya Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da UNDP Don Inganta Tsaro A Jihar Katsina

389
0

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Raɗɗa, ya sa hannu a
kan yarjejeniyar fahimtar juna da Hukumar Raya Ƙasa ta
Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP, domin ƙaddamar da cibiyar
bada kariya a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

An dai kulla yarjejeniyar ne a wani taro da ya gudana a ɗakin taro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja.

Ma’aikatar harkokin waje da ofishin jakadancin Norway ne ke ɗaukar nauyin shirin da nufin tallafa wa jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina.

Shirin dai ya na neman yin amfani da matakan bada kariya domin ƙarfafa matakan tsaro a yankin Arewa maso Yamma, da kuma yin amfani da tsarin sauyin yanayi da tsarin rayuwa mai ɗorewa domin kare tashe-tashen hankula a jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da rikici.

Da ya ke bayyana jin daɗin sa game da yarjejeniyar, Gwamna Raɗɗa ya ce shirin wani mabuɗi ne mai inganci da zai bude hanyar magance matsalolin tsaron da ke addabar jihar Katsina a halin yanzu.

Leave a Reply