Home Home PDP Ta Gargaɗi Mambobin Ta Na Majalisa Cewa Tilas Su Riƙa Yi...

PDP Ta Gargaɗi Mambobin Ta Na Majalisa Cewa Tilas Su Riƙa Yi Wa Jam’iyya Biyayya

150
0

Shugaban Riƙo na Jam’iyyar PDP Umar Damagum, ya ja kunnen zababbun ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP 116, cewa dole ne su yi wa jam’iyyar ta kai su wannan matsayin biyayya.

Damagum ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke ganawa da zababbun ‘yan majalisar a Abuja.

Taron, ya zo ne a daidai lokacin da yakin neman zaben shugaban majalisar da Mataimakin Kakakin sa ke ƙara zafi.

Jam’iyyar PDP dai ta na da wakilai 116, waɗanda zaɓen Kakakin Majalisa ya raba kawunan su.

Damagum ya ce, tabbas ya na sane cewa PDP ta na cikin rigingimu, amma ita da kan ta za ta iya magance matsalolin ta a cikin gida.

Leave a Reply