
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa, ya dage taron gangami na shiyyar Arewa maso Yamma da aka shirya yi a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu na shekara ta 2022.
Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar Bature ya sanya wa hannu.
Umar Bature, ya ce Kwamitin na sanar da dage taron gangami na shiyyar Arewa maso Yamma da aka shirya yi a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022, amma za a sanar da sabon kwanan wata a kan lokaci.
Duk da cewa jam’iyyar PDP ba ta bayyana dalilan dage taron ba zato ba tsammani ba, ana iya alakanta lamarin da zaben shekara ta 2022 na majalisar tarayya da za a yi a rana guda.













































