Home Labarai PDP Ta Ce Lai Ya Yi Ƙarya APC Ta Shiga Gwamnati Ba...

PDP Ta Ce Lai Ya Yi Ƙarya APC Ta Shiga Gwamnati Ba Tare Da Daftarin Ceto Nijeriya Ba

40
0

Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar, ta ƙaryata zargin da Gwamnatin Tarayya ta yi cewa Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Nijeriya na Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP ta kwafo shi ne daga daftarin APC.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Satumba ne Atiku Abubakar ya ƙaddamar da daftarin, wanda Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya yi wa martani da cewa babu komai a ciki sai shirnme da hauragiya kawai.

Sai dai rundunar yakin neman zaben Atiku Abubakar ta sake yin martani, inda ta ce ƙoƙarin kwatanta daftarin Atiku da hauragiyar da APC ta yi tsawon shekaru bakwai da sunan ayyuka almara ce kawai Ministan ke yi.

Sun ce kalaman Lai Mohammed rainin hankali ne ga Atiku da ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya, domin gwamnatin APC ta hau mulki ba tare da wata fallen takarda ko ɗaya mai ɗauke da daftarin tsare-tsaren yadda za ta ceto Nijeriya da tattalin arzikin ta ba, kuma saboda tsananin rashin shiri sai da aka shafe watanni shida kafin gwamnatin APC ta naɗa ministoci.