Home Home PDP, Labour Party Sun Taso Tinubu Gaba A Kan Jan Kafa Wajen...

PDP, Labour Party Sun Taso Tinubu Gaba A Kan Jan Kafa Wajen Bayyana Kadarorin Sa

294
0

An buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi koyi da marigayi Umaru Musa Yar’adua wajen bayyana kadarorin sa a idon duniya.

Kakakin jam’iyyar PDP na kasa Debo Ologunagba ya yi wannan kiran, inda ya ce ya kamata shugaba Tinubu da mataimakin sa su cika takardar da hukumar kula da ɗa’ar ma’aikata ta ba su domin bayyana kadarorin su, saboda doka ta buƙaci hakan.

Ologunagba ya ƙara da cewa, duk da sun maida takardun da ke dauke da kadarorin su, ya kamata a nuna shi a idon duniya kowa ya gani.

Sai dai Jam’iyyar Labour ta maida martini da cewa, ya kamata a ba Tinubu isashshen lokaci domin bayyana kadarorin sa, inda Shugaban jam’iyyar Julius Abure ya ce Tinubu hamshaƙin attajiri ne, don haka ya na buƙatar lokaci mai yawa kafin ya kammala haɗa kadarorin sa.

Leave a Reply