Home Labaru Ortom Ya Musanta Rahoton Cewa Shugaba Tinubu Ya Nada Shi A Matsayin...

Ortom Ya Musanta Rahoton Cewa Shugaba Tinubu Ya Nada Shi A Matsayin Minista

99
0

Tsohon gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya musanta
rahoton da ke yawo a shafukan yanar gizo cewa gwamnatin
Bola Tinubu ta sanya shi cikin waɗanda za ta naɗa Ministoci.

Rahotanni sun ce, tuni jihar Benue ta ɓarke da murna bayan jita-jitar ta karaɗe kafafen sada zumunta, cewa tsohon gwamnan ya shiga cikin mutanen da za su samu muƙamin minista.

Wata majiya ta ce, mutane da dama daga abokan siyasa da magoya bayan Samuel Ortom sun ɓarke da murna tare da taya shi murnar samun muƙami.

Sai dai a wata sanarwa da Samuel Ortom ya fitar a Makurdi ta hannun mai magana da yawun sa Terver Akase ya musanta jita-jitar.

Leave a Reply