Uwargidan shugaban kasa mai barin gado A’isha Buhari, ta mika ragamar mulkin ofishin ta ga matar zababben shugaban kasa Oluremi Tinubu.
An dai yi bikin mika mulkin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda A’isha ta mika wa Remi nauyin da ke kan kujerar, sannan ta mika mata muhimman takardu domin su yi mata jagora.
A’isha Biuhari, ta kuma mika tambarin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin Afrika ga magajiyar ta Remi, wadda a yanzu ita ce za ta zama babbar mai masaukin bakin duk matan shugabannin Afrika.
Duk da cewa aikin matar shugaban kasa ba ya cikin kundin tsarin mulki, amma A’isha Buhari ta nuna jin dadin ta a kan damar da aka ba ta na gudanar da ayyukan taimakon jama’a, da kuma hadin gwiwa da kungiyoyin agaji a tsawon shekaru takwas da ta yi a ofis.














































